Connect with us

News

Masu Zanga Zanga Sun Yi Wa Majalisar Dokoki Ta Kasa Tsinke Kan Kudirin Gyara Harajin Shugaba Tinubu

Published

on

Masu zanga zangar sun mamaye Majalisar Dokoki ta kasa kan kudirin gyara harajin Tinubu

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Wasu matasa ‘yan Arewa sun gudanar da zanga-zanga a ƙofar shiga majalisa a ranar Talata domin jan kunnen masu tsagin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa, sanata Barau Jibrin, kan yunƙurin da suke na mara ƙudurin dokokin haraji baya wanda shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Advertisement

Masu zanga-zangar dai na riƙe da kwalaye waɗanda aka yi rubutu a kansu da ke cewa, “ku rabu da sanata Barau,” da “Sanata Barau mai kishin al’umma ne,” da “ku daina sukar sanata Barau” da “Sanata Barau shi ne jagora a Arewa,” sai kuma “Sanata Barau shi ne Sardauna na wannan zamanin”.

Gwamnati Za Ta Fara Yi Wa Yara Allurar Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro

Sanata Barau dai ya fuskanci suka mai ƙarfi daga wasu sassan Arewacin Najeriya tun bayan gabatar da ƙudurin sake fasalin haraji wanda majalisa ta fara nazarinsa.

Advertisement

Mataimakin shugaban majalisar shi ne mai wakiltar Kano ta Arewa wanda ya jagoranci zaman majalisar da aka yi a ranar Laraba a lokacin da kwamitin kuɗi da sake fasalin haraji na fadar shugaban ƙasa ya bayyana a gaban majalisar suka domin yi wa majalisar ƙarin haske kan ƙudurorin.

A ranar ne kuma wasu daga cikin ‘yan majalisar, musamman sanata Ali Ndume daga jihar Borno da takwaransa, sanata Abdul Ningi, suka yi ƙoƙarin hana kwamitin kuɗin bayyana aka gaban majalisar.

Advertisement

Wannan al’amari ya jawo muhawara mai zafin gaske a majalisar wanda har wasu daga cikin ‘yan majalisu daga Arewa suka yi ƙoƙarin ficewa daga majalisar, amma daga baya suka fasa.

Sai dai har zuwa wannan lokaci, mataimakin shugaban majalisar bai fito ya bayyana ra’ayinsa game da wannan ƙuduri ba, duk da ana zargin cewa yana nuna goyon bayansa ne.

Advertisement

Ƙudurin dokokin dai sun tsallake karatu na biyu a majalisar a ranar Alhamis inda aka miƙa ƙudurin ga kwamitin kuɗi na majalisar wanda sanata Sani Musa daga jihar Neja ke jagoranta domin cigaba da bin matakan da suka kamata kamar na jin ra’ayin al’umma.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kuma ba da umarni ga kwamitin da ya shigo da majalisar tattalin arziƙin ƙasa da ƙungiyar gwamnonin Arewa da ƙungiyoyin fararen hula cikin taron jin ra’ayin al’umma. Har zuwa yanzu dai kwamitin bai sanya ranar da za a gudanar da taron ba.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending