Connect with us

News

Rundunar ’Yan Sanda Ta Dakatar Da Jami’anta Da Ga Aiki Saboda Satar Sama Da Naira Miliyan 43

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a ranar Laraba ta sanar da dakatar da jami’anta guda hudu da aka samu da laifin satar Naira miliyan 43.16 daga cikin Naira miliyan 74.95 da aka kwato a wani kamen da ba a amince da shi ba a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi, ne bayyana hakan a cikinwata sanarwa ya fitar.

Emefiele Ne Ya Mallaki Rukunin Gidaje 753 Da Hukumar EFCC Ta Ƙwace A Abuja 

Sanarwar ta kara da cewa da jami’an da abin ya shafa su ne DSP Peter Ejike, Insfekta Ekende Edwin, Insfekta Esther Okafor, da Sajen Talabi Kayode.

Advertisement

An same su da laifin hada baki wajen lalata kayayyakin shaidar tuhuma, cin zarafin ofis, da wasu munanan halaye na rashin da’a.

A cewar Adejobi, jami’an, karkashin jagorancin Insfekta Okafor da kuma umarnin DSP Ejike, sun kama Andrew Ejah, ma’aikacin FATFAD Cargo Nigeria Limited, wanda ke jigilar kudaden ne a madadin wasu abokan hulɗa a watan Agustan 2023.

Advertisement

An zargi jami’an da bayar da rahoton cewa sun kwato Naira miliyan 31.79 kawai, suna ɓoye sauran Naira miliyan 43.16. Bayan korafin da masu kudin suka shigar, an mayar da lamarin zuwa Sashen IGP Monitoring Unit.

A yayin binciken, an kwato adadin Naira miliyan 31.79 daga hannun jami’an, wadanda suka yi ikirarin cewa wannan ne kawai kudin da suka kwato daga hannun Andrew Ejah yayin kamun sa.

Advertisement

“Bayan bincike mai zurfi da kuma jerin shari’o’i a gaban kwamitin ladabtarwa, an gano cewa jami’an sun dauki hotunan wanda ake zargi da buhunan kudin a lokacin kamun, amma suka yi ikirarin cewa wayar da suka yi amfani da ita ta lalace kuma ta bace, don kokarin boye laifinsu.

Ya kara da cewa sun yi amfani da dabaru daban-daban don rufe laifinsu, ciki har da yada labaran karya da bayanai marasa tushe ga wasu kafafen labarai na yanar gizo da jaridu.

Advertisement

“An dakatar da wadannan jami’ai bayan an same su da laifukan rashin da’a masu tsanani, lalata kayayyakin shaidar tuhuma, cin zarafin ofis, cin hanci da rashawa, gudanar da aikin da ba bisa ka’ida ba, da kuma halayen da ba su dace da jami’in ‘yan sanda ba,” in ji sanarwar.

Adejobi ya yi Allah-wadai da abin da ya kira “yunkurin yada bayanan karya” da nufin hada sunan Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da wannan rikicin.

Advertisement

Har ila yau, ya musanta zarge-zargen da ke cewa Sufeto-Janar din na boye wata kungiyar da ake zargi da safarar sabbin takardun kudi daga Babban Bankin Najeriya.

NIGERIAN TRACKER 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending