News
Gwamnatin Kano Zata Cigaba Da Karbar Haraji A Wajen Yan Adaidaita Sahu.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin ta na dawo da karbar haraji daga hannun matuka baburan Adaidaita Sahu a jihar.
Kwamishinan Sufuri na Jihar Muhammad Ibrahim Diggol, ne ya bayyana hakan, yayin tattaunawarsa da Kafar yada Labarai ta HIKIMA RADIYO, a shirin su mai suna Hannu Daya.
Tabbas Mu Muke Jefa Kawunan Mu Cikin Matsaloli —Imam Murtadha Muhammad Gusau
Tun a kwanakin baya Gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf, ta sanar da cewa zata dawo karbar harajin, amma abin ya lafa sakamakon wasu dalilai.
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ne ya kirkiro karbar haraji daga hannun masu haya da baburan Adaidaita Sahu.
A lokacin da ake karbar harajin an rika samun sabani tsakanin masu Adaidaita Sahu da jami’an hukumar kula da zarga zargan cunkoson ababen hawa ta Kano, KAROTA wanda sune masu alhakin tabbatar da biyan harajin.
Lokacin karbar harajin kowanne Matukin Adaidaita Sahu yana biyan naira 100, a kowacce rana in har ya fito aiki.
