Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Shirin Ta Na Fara Karbar Haraji Daga Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar

Published

on

DAGA  NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin ta na fara karbar haraji daga ma’aikatar lafiya ta jihar.

Advertisement

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya sanar da hakan a yau bayan ya kammala kare kasafin kudin ma’aikatar sa na shekarar 2025, a zauren majalisar dokokin Kano.

Manyan Motocin Daukar Kaya Za Su Daina Shigowa Kano Da Rana — Gwamnatin Kano

A cewar sa ma’aikatar zata tattara harajin ne daga asibitocin jihar, wanda hakan zai fara aiki daga shekara mai kamawa.

Advertisement

Ya kara da cewa sun fahimci akwai bangarorin da za’a iya samarwa gwamnati kudaden shiga a fannin asibitocin.

Matsin tattalin arziki da ake fuskanta dai na daga cikin dalilin da yasa gwamnatoci nemo hanyoyin da zasu kara samun kudaden shiga, yayin da al’umma ke kokawa akan tsadar rayuwa, musamman saboda wasu manufofin gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending