News
Kungiyar Alkalai Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Alkalan Najeriya (MAN), reshen jihar Cross River, ta shiga yajin aikin sai baba ta gani bayan kasa cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.
Za a fara yajin aikin ne a yau, Litinin, 9 ga Disamba, 2024, inda aka umarci dukkan alkalan jihar da su daina gudanar da duk wani aikin ofis, ciki har da zaman kotu, har sai wani karin bayani ya zo.
NAFDAC Ta Gargaɗi Masu Burodi Kan Amfani Da Sakarin Wajen Yin Burodinsu
Wannan bayanin yana cikin wata sanarwa mai taken ‘Bulletin No. 2: Indefinite Strike’ da Shugaban MAN na reshen Cross River, Godwin Onah, da Sakatare Janar, Solomon Abuo, suka sanya wa hannu, kuma aka gabatar wa manema labarai jiya a Calabar.
Jaridar GUARDIAN ta ruwaito cewa ma’aikatan shari’a sun bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnati a ranar 5 ga Nuwamba, 2024, don gargadin fara yajin aiki a ranar 27 ga Nuwamba.
Sun fara yajin aiki na gargadi na tsawon kwanaki uku domin jaddada bukatunsu guda takwas ga gwamnatin Bassey Otu.
A cewar sanarwar, rashin cika bukatun kungiyar daga bangaren gwamnati ne ya sa aka fara wannan yajin aiki.
Bukatun sun hada da karin albashi da wasu batutuwan jin dadin aiki guda bakwai.
