News
Kotu Ta Ce Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar Rusau Naira Biliyan 8.5
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babbar kotun jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya biya kamfanin Lamash Properties diyyar Naira Biliyan 8 da miliyan 511.
Haka zalika kotun ta ma ce kudin da kamfanin ya kashe wajen dauko lauyoyi da sauran kunji-kunji da ya kai Naira miliyan 10 shima gwamnatin jihar Kano ce za ta biya kamfanin saboda rushe ginin kamfanin da ke tsohuwar Daula Hotel ya sabawa kaida saboda kamfanin ya bi ka’ida a hukumance wajen mallakar kaddarar daga gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
DA DUMI-DUMI: Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Litar Man fetur
In za a iya tunawa kwanaki can a karshen shekarar da ta wuce ta 2023, babbar kotun tarayya da ke Kano ta umarci gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya masu kadarori a filin IDI diyyar sama da Naira Biliyan 30.
Yanzu dai ya rage wa gwamnatin jihar Kano ta daukaka kara zuwa kotuna na gaba, don ganin ko za ta iya soke hukuncin kotunan na baya
Muddin ta gaza kuwa to sai an kwashe kudin jihar Kano Naira Biliyan 40 an biya wadannan mamallaka kadarorin.
