News
KASAFIN KUDIN 2025: Tayoyin Motocin Fadar Shugaban Kasa Da Gina Ofisoshi Za Su Lakume Naira Biliyan 15
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gidan Gwamnati ya ware Naira biliyan 15.09 don siyan tayoyin motoci masu kariya daga harsashi, motoci na Sport Utility Vehicles (SUV), motoci na aiki, da sauran motoci, da kuma gina wani ofisoshi na mataimaka da masu baiwa shugaban kasa shawara.
Hakama an ware naira biliyan 5.49 domin gyare-gyare a fadar ta shugaban kasa cikin shekara daya.
Kotu Ta Ce Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar Rusau Naira Biliyan 8.5
Wadannan bayanan dai na kunshe a cikin kasafin kudin shekara ta 2025 da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar, wanda aka fitar da bayanan ga al’umma a yau Alhamis kamar yanda Jaridar PUNCH ta ruwaito
Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudi mai taken “Kasafin Kudi na Sabuntawa: Tsare Tsaro, Gina Arziki” a taron hadin gwiwar Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai a ranar Laraba, yana gabatar da shirin kashe kudi na Naira tiriliyan 49.70.
Kasafin kudin ya mayar da hankali kan tsaro, abubuwan more rayuwa, da ci gaban Tattalin Arziki na mutane,
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
