News
Jami’an Hukumar DSS sun kama Mahdi Shehu
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Jami’an Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama wani sharhi kan harkokin siyasa mazaunin Kaduna Mahdi Shehu.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa An kama Shehu ne a karshen mako a kan wani faifan bidiyo na bogi, da ke iyaka da batun tsaron kasa, wanda ya yi ta yaduwa.
Muhadi Shehu ya watsa wani tsohon faifan bidiyo a shafukan sada zumunta kuma ya na zargi gwamnatin tarraya da shirin kafa sansanin sojin Faransa a yankin Arewa maso Yamma.
DATELINE NIGERIA ta rahoto cewa tsohon babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN) a watan Fabrairun wannan shekara ya bayyana yadda ake zargin Shehu kan yunkurin karbar kudi.
Shehu ya yi ikirarin ta bakin lauyansa, Mohammed Abubakar, cewa an kama shi ne saboda kiran Shugaba Bola Tinubu da ya binciki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan jami’an sa.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
