Connect with us

News

Aƙalla Mutum 71 Ne Suka Rasu Ya Yin Da Babbar Mota Cike Da Fasinjoji ‘Yan Biki Ta Kife Cikin Kogi

Published

on

wata babbar mota cike da fasinjoji ‘yan biki ta kife cikin kogi

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Aƙalla mutum 71 ne suka rasu a Ethiopia a lokacin da wata babbar mota cike da fasinjoji ta faɗa a cikin kogi, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin yankin Sidama da ke kudancin ƙasar ya tabbatar.

Advertisement

Hatsarin wanda ya laƙume rayukan maza 68 da mata uku, ya faru ne a ranar Lahadi a gundumar Bona, kamar yadda sanarwar da aka fitar ranar Lahadi da dare ta bayyana.

Akalla Kaso 53.9 Cikin 100 Na Yara A  Najeriya Na  Fama Da Tsananin Fatara Da Yunwa – Rahoto 

Wosenyeleh Simion, wanda shi ne mai magana da yawun gwamnatin yankin Sidama ya bayyana cewa fasinjojin baƙi ne waɗanda za su je wurin biki, inda wasu iyalan suka rasa mutane da dama.

Advertisement

Shi ma gidan talabijin na Ethiopia EBC ya ruwaito cewa fasinjojin suna hanyar zuwa wuri biki a lokacin da hatsarin ya faru.

 

Advertisement

Reuters

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending