News
Akalla Kaso 53.9 Cikin 100 Na Yara A Najeriya Na Fama Da Tsananin Fatara Da Yunwa – Rahoto

DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Wani rahoto game da halin da yara ke ciki (SitAn) a Najeriya ya bayyana wasu dalilai da ya sa yara kaso 53.9% ke fama da matsaloli daban-daban da suka shafi talauci.
Wannan rahoto an ƙaddamar da shi ne a yayin bikin ranar yara ta duniya ta 20 ga watan Nuwambar 2024 wanda da gwamnatin Najeriya tare da taimakon asusun tallafa wa ƙananan yara ta duniya (UNICEF) suka shirya domin gano ƙalubalen da yara ke fuskanta a Najeriya.
A cewar wannan rahoto, cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da rashin mai da hankali daga masu mulki da tashe-tashen hankula saboda ayyukan ta’addanci da rashin wadataccen zuba jari ga ɓangarorin gina ɗan’Adam su ne muhimman abubuwa da suka jefa yara cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Sannan rahoton ya ce, raba al’umma da gidajensu da sake neman wurin zama ya ƙara jefa yara cikin mawuyacin hali a Najeriya.
Hakazalika, rahoton ya bayyana talaucin ƙananan yara da cewa, “wani yanayi ne da yara ke samun kansu na ƙarancin abubuwa inganta rayuwa da kwanciyar hankali da zai tabbatar da sun rayu, sun samu cigaba da kuma nasara.
Kuma rashin waɗancan abubuwa na tauye musu ‘yancinsu da ba su damar shiga a dama da su a rayuwar kamar sauran mutane.”
Rahoton ya bayyana wasu ma’aunai guda bakwai da ake kalla wajen tantance yara na fama da talauci ko ba sa fama da shi ta hanyar la’akari da wadatar damar samun kulawa ta lafiya da ruwan sha da tsabta da abinci mai gina jiki da wurin kwana da ilimi da kuma samun bayanai.
Game da Alƙaluman Nazarin Matakan Talauci (MPI), rahoton ya ce, akwai ‘yan bambance-bambance da ake samu a tsakanin jihohin Najeriya 36 ciki har da babban birnin tarayya Abuja.
Ga misali, a cewar rahoton, jihar Osun ita ce mafi ƙarancin yaran da ke cikin talauci da kaso 17.5%, matakin rashin abubuwan inganta rayuwa ya kama kaso 35.3% inda Cibiyar Nazarin Alƙaluman Gina Ɗan’Adam (HDI) ta ayyana jihar a matsayin ta 14 a Najeriya.
“A jihar Sakkwato kuwa, alƙaluman talaucin yara ya nuna su ne kan gaba da kaso 89.9%, inda matakin rashin abubuwan inganta rayuwa ya kai kaso 50.4% sannan HID ta ayyana jihar a matsayi na 37%.”
“A jihar Lagos, alƙalumar samun talaucin yara ya kai kaso 27.8% inda matakin rashin abubuwan more rayuwa ya kai kaso 36.8% sannan HID ta ba ta kaso 1%.”
A cewar rahoton yaran da ke ƙarƙara da suke fama da talauci sun kai kaso 65.7% inda a birane suke da kso 29.7%.
Rahoton ya ce, jihar Sakkwato (80.4%) da Kebbi (74.9%) da Zamfara (74%) su ne kan gaba da yaran da ke cikin mummunan halin talauci a Najeriya.
“A ɗaya hannun kuwa, yara ƙasa da kaso 20% ne a jihar Edo (19%) da jihar Legas (17.3) ke fama da matsalar talauci.”
“Yaran da suke Sakkwato sun fi neman abu su rasa da kaso 74.1% idan aka kwatanta da yaran da suke jihar Legas da ke da kaso 57.7%.
Sannan rahoton gidajen da suka fi yawan iyali ko yara su ne suka fi gamuwa da matalar talaucin yara idan aka kwatanta su da gidajen da ke da yara kaɗan.
Binciken ya kuma nuna cewa gidajen mazan gidan (masu gida) ko uwayensu suke ba su da ilimi an fi samun matsalar yaran da ke fama da talauci idan aka kwatanta da gidajen da iyayen yaran suke da ilimi daga matakin sakandare zuwa ilimi a matakin manyan makarantu.
Kuma yaran da iyayensu mata ba su da ilimi sun fi fama da wannan matsala idan aka kwatanta da waɗanda iyayensu ke da ilimi.
“Sannan za a iya cewa yara almajirai su ne suka fi kowanne yaro fama da matsalar talaucin rashin abin yara ke buƙata domin kyakkyawar rayuwa.”
“Irin waɗancan yara (almajirai) na kan gaba wajen nema abin da za su ci – sun rasa kyakkyawan yanayin rayuwa da abinci mai gina jiki da ruwan sha da tsabta da samun kiwon lafiya da ilimi da kulawar iyaye.”
“Sannan sun rasa samun kariya daga take haƙƙi da cin zarafinsu da shiga lamuran da suka shafi rayuwarsu kuma mafi yawansu sukan samu kansu a halin yin aikatau da kuma cin zarafi.”
“Ana kuma amfani da irin waɗannan yara a lokutan tashe-tsashen hankula wajen ɗaukar makami.”
Domin magance matsalar, rahoton ya ba da shawarar akwai buƙatar mahukunta su taka rawa.
Iyaye da masu kula da yara su ma akwai buƙatar su ba da gudunmowa wajen magance matsalar talaucin ƙananan yara da ba su kariya.
Rahoton ya kuma lura cewa yaran da ke fama da talauci sun dogara ne da asibitoci da makarantu da sauran cibiyoyin hidimta wa al’umma na gwamnati da sauransu.
Don haka, akwai buƙatar hukumomi da shirye-shiryen da suke yi ya kamata a tsara su ta yadda yara za su iya cin moriyarsu.
“Ingantaccen shugabanci a kowanne mataki zai taimka wajen fidda tsare-tsare managarta da amfani da rarraba kowanne irin tallafi na gina al’umma yadda ya kamata da rage talauci da marawa kare haƙƙin yara baya.”
“Akwai buƙatar gwamnati ta tallafa wa iyalai ta hanyar ba su mafi ƙarancin abin da za su iya rayuwa da shi domin magance matsalar tattalin arziƙi daga ba wa yara damar cika muradansu.”
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa an wallafa wannan rahoto na farko ne a shekarar 2022 wanda a matakin farko ya gudanar da bincikensa kan iyalai daga ɓangarori da dama na tattara alƙaluma.
Sai kuma a 2024 da aka sake inganta binciken tare wallafa shi domin tallafa wa gwamnatin wajen fitar da tsare-tsarenta ta yadda zai ƙunshi zuba jari wajen inganta rayuwar yara.
Premium Times
