Connect with us

News

Mun Kama Masu Kwacen Wayoyi 1372, Da Masu Fadan Daba Sama Da 3000 — Anti Snatching Force 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar tsaron nan da ke yaki da fadan Daba da kwacen Waya da kawar da harkokin Shaye-shaye ta Anty Snaching Phone da ke nan Kano, ta ce daga farkon watan Afrilun 2024, kawo yanzu ta samu nasarar cafke wadanda ake zargi da kwacen wayoyi su 1372, tare da kama wadanda ake zargi da fadan Daba sama da mutum dubu uku, da dai sauran laifuka.

Advertisement

Mai Magana da yawun rundunar Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da rundunar ta gudanar a hedikwatar ta da ke unguwar Saharada, ya ce sun samu nasarar ne a cikin watanni takawas da suka gabata, duk kuwa da irin kalubalen da suke fuskanta na kayan aiki.

Jami’an Hukumar DSS sun kama Mahdi Shehu

Ya kuma ce rundunar karkashin jagorancin Inuwa Salisu Sharada, ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da fadan Dabar da kuma masu kwacen wayar ne a unguwanni daban-daban a sassan jihar nan, domin dakile miyagun ayyukan nasu a jihar nan don kara wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Advertisement

Ibrahim Garba Ahmad ya kuma ce sun samu nasarar cafke wasu ‘yan mata a wuraren da ake yin abubuwan da basu kamata ba, bisa zargin su da yada badala, tare kuma da kama wadanda ake zargi da satar wayar wayar fitilun kan titi wato Amo Cable, da kuma baburin Adai-dai ta sahu dukka a cikin wannan shekarar.

Sai dai kuma ya bayyana cewar duk da irin wannan kokari nasu amma da mota daya suke aiki, sai dai idan za su fita da yawa jami’ansu su hau baburan adai-dai ta sahu domin fita aiki.

Advertisement

Kasancewar rundunar na karkashin kwamitin tsaron da gwamnatin jihar Kano ta kafa, a don haka ne muka zanta da shugaban kwamitin Janar Gambo Ahmad mai Adu’a, mai ritaya, inda ya ce tuni aka shirya domin magance kalubalen da jami’an ke fuskanta

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da fadan Daba ya damu al’umma musamman ma a cikin unguwannin kwaryar birnin Kano, a baya-bayan nan, al’amarin da mutane ke ci gaba da buƙatar ganin jami’an tsaro sun matsa lamba wajen magance matsalar don kara wanzuwar zaman lafiya

Advertisement

a jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending