News
Na Ba Da Hayar Gida Na Da Ke Kaduna Domin In Samu Kudin Da Zan Rika Ciyar Da Iyali Na —Buhari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Advertisements
Advertisements
Tsohon shugaban kasar na Nigeria ya ce bai saci ko sisin kwabo mallakin Najeriya ba, tsawon shekaru 8 da ya yi yana mulk.
Advertisements
‘Ko a yanzun nan haka ina rayuwa ne bisa kudin da na karba daga hayar daya daga cikin gidaje na biyu da ke Kaduna. Gidaje 3 na mallaka, daya a nan Daura mahaifata guda biyu a Kaduna, na dauki daya daga cikin na Kadunan na bada hayarsa domin samun kudin da zan yi bukatu ga iyali na” inji tsohon shugaban kasar na Najeriya.
Advertisements
Advertisements
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a gidan gwamnatin jihar Katsina.
Advertisements
