News
An Dakatar Da Sheikh Bin Uthman Daga Limancin Masallacin Sahaba, DSS Ta gayyace shi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamitin kula da Masallacin Sahaba da ke Kano ya dakatar da fitaccen Malamin nan Sheikh Bin Uthman daga Limanci a Masallacin sakamakon zarginsa da rura wutar sabani game da jagorancin Masallacin.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci Shehin Malamin kan wannan batu, inda ta bukace-shi da karya gudanar da huduba ko furta wata kalma da za ta tunzura magoya baya su tada zaune tsaye.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa, tun a washegarin faruwar hatsaniyar da ta faru a Masallacin ne hukumar kula da Masallacin ta tura wa Shehin Malamin da takardar dakatar wa, inda a ranar litinin kuma hukumar tsaron DSS da Council of Ulama suka zauna da Sheikh Bin Uthman, har ma bayanai sun ce Council of Ulama sun shawarci Sheikh Bin Uthman da ya hakura da wannan sabon Masallacin ya koma tsohon Masallacin sa na Sahaba domin ci gaba da Limanci acan.
