Connect with us

News

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu bakin gilas shiga harabarsa

Published

on

A asibitin Aminu Kano likitoci suka cire min mahaifa da Jaririna ba tare da sanina ba Maimunat Ibrahim da ga Kano

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

 

Advertisement

A wani mataki na tsaro da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, da ke jihar Kano ya dauka domin magance barazanar tsaro da yake fuskanta, mahukuntan asibitin sun fara aiwatar da dokar hana motocin da ke da baƙin gilashi (tinted glass) shiga harabar asibitin.

A cewar mahukunta, wannan mataki na da nufin tabbatar da tsaro ga marasa lafiya, ma’aikata da dukkan al’ummar da ke amfana da ayyukan asibitin. Sun bayyana cewa, motocin da ke dauke da marasa lafiya ko ma’aikatan asibitin za su iya shiga, amma sai sun bi ka’idojin tsaro na musamman da aka gindaya.

Advertisement

Ba Mu Fara Daukar Sabbin Ma’aikata Ba  — Shugaban Hukumar KAROTA 

A wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na asibitin, Usman Rabiu Mudi ya fitar, ya ce, an kafa dokar hana motocin masu baƙin gilashi shiga ne saboda wasu munanan abubuwan da suka faru.

Ya bayyana irin munanan ababen kamar yunƙurin sace mutane ta amfani da irin waɗannan motocin da kuma aikata ayyukan laifi daban-daban da suka ƙunshi sata da aikata abubuwan da ba su dace ba a cikin harabar asibitin.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa, ma’aikatan asibitin da ke amfani da mota za su yi rajistar motocinsu a ofishin tsaro don samun tambarin tantancewa da izinin shiga.

Asibitin na kira ga jama’a da su bada hadin kai wajen bin wannan sabon tsari, domin tabbatar da zaman lafiya da kariya ga rayuka da dukiyoyi a harabar asibitin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending