News
Zargin Rashawa: Jami’in Binance Ya Ambaci Wasu ‘Yan Majalisar Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Shugaban sashen tsaron Binance, Tigran Gambaryan, ya zargi wasu ‘yan majalisar wakilai guda uku da neman cin hanci na dala miliyan 150 daga hannunsa domin hana shari’ar da ake yi masa a Najeriya.
A cewar Gambaryan, ‘yan majalisar da ake zargi sun hada da Peter Akpanke, Philip Agbese, da Ginger Obinna Onwusibe, dukkansu daga majalisar wakilai. Ya bayyana hakan ne ta kafarsa ta X, inda kafofin yada labarai a Najeriya suka ruwaito zargin nasa.
Mutane 23 Sun Rasa Rayuka, 48 Sun Jikkata A Mummunan Hatsarin Tirela A Kano
Wannan batu na kara jaddada damuwar da ake yi kan zarge-zargen da ake wa wasu manyan jami’an gwamnati na taimakawa masu laifi ko kuma wasu ‘yan kasashen waje wajen zambatar Najeriya.
Muna ci gaba da bibiyar lamarin don samun karin bayani kan wannan zargi da kuma martanin da ‘yan majalisar da aka ambata za su bayar.
