Connect with us

News

Mutum 80 Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Hadarin Jirgin Sama A Toronto

Published

on

Mutum 80 Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Hadarin Jirgin Sama

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Babban jami’in hukumar kashe gobara na birnin Toronto, Todd Aitken, ya bayyana cewa mutum 18 daga cikin fasinjojin sun samu raunuka a hadarin jirgin da ya taso daga Minneapolis, Amurka, zuwa Kanada.

Advertisement

Mai rikon mukamin Magajin Garin Toronto, Olivia Chow, ta ce ta yi matukar firgita da jin labarin hadarin, amma ta samu kwanciyar hankali bayan tabbatar da cewa dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin – kimanin mutum 80 – sun tsira da ransu. Ta bayyana hakan a shafinta na X.

Jami’ar Al-Istiqama Ta Sanar da Ranar Bikin Yaye Dalibai Na 2025 A Yayin Da Makarantar Ke Daukar Matakan Inganta Ilimi

Wannan hadari ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da yawaitar hadurran jiragen sama a arewacin Amurka. A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, wani jirgin helikwafta na soji ya yi taho mu gama da jirgin fasinja a birnin Washington, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 67.

Advertisement

Haka kuma, wani jirgin daukar marasa lafiya ya fadi a Philadelphia, inda mutane bakwai suka rasa ransu, sai kuma wani hadarin jirgin sama a Alaska da ya halaka mutum 10.

Ko da yake ba a rasa rai a hadarin jirgin na Toronto, lamarin ya kara jaddada bukatar tsaurara matakan tsaro a harkokin sufurin jiragen sama.

Advertisement

 

 

Advertisement

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending