Connect with us

News

Yan’Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaron Sa Kai 6 A Sokkota 

Published

on

1740049377194

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Yan bindiga sun kashe jam’an tsaron sa kai shida 6 a lokacin da suka kai taimako a wani farmaki da yan bindigar suka kai  Kamarar Hukumar Sabon Birni ta Jihar sokkota.

Advertisement

Aminiya ta rawaito jami’an sun gamu da ajalinsu ne a ya yin da yan bindigar suka yi musu kwanton ɓauna lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma .

Rahotanni sun bayyana cewa abokin aikinsu ne ya kira ya sanar da cewa, ’yan bindiga suna hanyarsu ta kawo hari ƙauyensi da ke kusa da Unguwan Lalle.

Advertisement

“Jami’an tsaron sun nemi abin hawa daga hukumar karamar hukumar amma an hana su, saboda an hana su gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum su kaɗai ba tare da jami’an tsaron gwamnatin ba,” in ji majiyar.

Da ba su samu abin hawa ba, sai suka hau baburansu suka tafi ƙauyen, amma aka yi rashin sa’a, ’yan bindigar sun Riga da sun yi musu kwanton ɓauna.

Advertisement

Sai dai kafin yan bindigar su kashe mute ne 6 sai da suka yi musayar wuta da ’yan ta’adda.

Lokacin da aka tuntube ,kwamandan Rundunar Tsaro ta Sakkwato, Kanar Na-Allah Idris, ya ƙi cewa komai kan harin.

Advertisement

Haka nan, shugaban majalisa, Alhaji Ayuba Hashimu da memba mai wakiltar Sabon Aminu Boza sun kasa amsa kiran wayar wakilinmu.

An tuntuɓi kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rafa’i, inda ya ce ba shi da rahoto kan lamarin.

Advertisement

Mai ba da shawara na musamman ga gwamna Ahmed Aliyu Ahmed kan sha’anin tsaro, Ahmed Usman ya tabbatar da harin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending