Connect with us

News

Zargin Ta’addanci : Taimakawa Nageriya Mu Ke Yi Ba Daukar Nauyin Boko Haram  Ba – Amurka 

Published

on

boko haram

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kasar Amurka ta ce ba bu wata hukuma a ‘kasar ta dake daukar nauyin ta’addancin kungiyar Boko Haram a Nageriya kamar yadda dan majalisssar Amurka ,Scortt Perry ya yi iƙirari.

Advertisement

Jakadan Amurkan a Najeriya, Richard M. Mills Jr. shi ne ya kawar da wannan zargi a gaban manema labarai jim kaɗan bayan wata ganawar sirri da ya yi tare da gwamnonin jihohin Najeriya 36.

Ya ce Amurka ba ta da hannu a ƙungiyar Boko Haram, hasali taimakawa Najeriya keyi  don ganin ta kawar da matsalolin tsaro da ta adddabeta.

Advertisement

Tun da farki ɗan Majalisar Amurka na jam’iyyar Republican da ke wakiltar Pennsylvania, Scott Perry ya yi iƙirarin cewa hukumar raya ƙasashe ta Amurka USAID ce ke ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta’addanci a ƙasashe ciki har da Boko Haram ta Najeriya.

A ƙoƙarinsa na kare manufar shugaba Donald Trump game da rushe hukumar USAID, Scott ya ce kaso mai yawa na kuɗin da ake tattarawa da sunan tallafi suna ƙarewa ne a hannun kungiyoyin ta’addancin irinsu boko haram da ISIS da Al-Qaeda .

Advertisement

Ƙungiyar ta’addancin ta Boko haram ta shafe tsawon shekaru aƙalla 15 a yankin arewa maso gabashin Najeriya da wasu sassa na Chadi da Nijar da Arewacin Kamaru da kuma Mali.

Premium Times News

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending