Connect with us

News

Gobara Ta ‘Kone Gidaje Da Asarar Dukiya Mai Yawa A Kano  

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, inda ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gobarar ta tashi ne a sakamakon wata wuta da aka yi amfani da ita wajen dafa abinci, amma aka bar ta ba tare da an kashe ba.

Cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, ya ce gobarar ba ta yi asarar rayuka ba amma ta janyo asarar  Dukiya mai tarin yawa.

Advertisement

mazauna yankin sun kai daukin gaggawa domin ceton rayuka da dukiyoyinsu.

Tuni dai Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin, inda suka bayyana cewa gobarar ta lalata gidaje guda shida, kaya, hatsi, dabbobi da kuma wasu kayayyakin amfanin yau da kullum da darajarsu ta kai ta miliyoyin Naira

Sarkin ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa kuma ya ba su tallafin Naira 200,000 domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *