News
KAROTA Ta Yi Kira Ga Direbobi Da Su Yi Tuki Cikin Hankali A Lokacin Azumin Ramadan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Yayin da ake shirin shigowa cikin watan Ramadan mai alfarma, Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) na yin kira ga dukkan masu ababen hawa musamman direbobi da su yi hakuri tare da tuki cikin natsuwa da taka tsantsan.
Wannan wata na ibada kan kawo sauyi a halayen tuki saboda gajiya, rashin ruwa a jiki da cunkoson ababen hawa musamman lokacin Iftar da sallar Taraweeh.
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Samu Yabo Kan Gyara Da Inganta Asibitoci A Kano
Domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, KAROTA na baiwa direbobi wadannan shawarwari:
Guji Gudun Wuce Kima Kafin Iftar: Yawan gaggawar komawa gida don yin buda baki kan haddasa hatsari. Ku yi tuki cikin sauri mai tsaka-tsaki domin kare kanku da sauran masu tafiya.
Yi Hakuri da Kyautata Mu’amala: Cunkoso kan karu a kasuwanni da kusa da masallatai, don haka a kaucewa tuki barkatai da nuna hakuri ga sauran jama’a.
Guji Tuki Idan Kuna Jin Gajiya: Azumi kan haddasa gajiya ko jiri. Idan kun ji kasala, ku dakata kafin ku ci gaba da tafiya.
Ku Kasance Cikin Shiri: Ku shirya tafiyar ku da wuri domin kaucewa lokacin cunkoso.
Kula da Masu Tafiya a Kafa da Masu Keke: Da dama kan yi tafiya zuwa masallatai, musamman da daddare. Ku yi tuki cikin taka tsantsan a wuraren da ake cunkoso.
Bin Dokokin Hanya da Umarnin Jami’an KAROTA: Yin biyayya ga dokokin hanya zai taimaka wajen kare rayuka da rage hadurra.
Hukumar KAROTA na ci gaba da jajircewa wajen kare lafiyar jama’a a duk lokacin azumi tare da kara yawan sintiri domin tabbatar da ingantaccen zirga-zirga a cikin birni.
Daraktan Hukumar, Hon. Faisal Mahmud Kabir, na taya al’ummar musulmi murna tare da yi musu fatan Allah ya karbi ibadunsu, ya ba da zaman lafiya da tsaro a wannan wata mai alfarma.
