News
Kungiyar Yan Jaridu Ta Yabawa Dan Majalisa Rurum Bisa Tallafawa ‘Ya’yanta A Lokacin Azumin Ramadana
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar ‘Yan Jarida da Masu Buga Labarai a yanar gizo ta Northern Online Media Group (NORP), reshen Jihar Kano, ta jinjinawa wakilin mazabar Rano, Kibiya, da Bunkure a Majalisar Tarayya, Hon. Kabiru Alhassan Rurum, saboda Kyautatawar tallafin buhunan shinkafa na kilogiram 25 da ya bai wa kowane memba a matsayin kyautar Ramadan.
A cikin wata sanarwa da shugaban rikon kwarya na kungiyar, Comrade Abbas Yusha’u Yusuf, ya sanya wa hannu, NORP ta bayyana cewa wannan kyauta wata alama ce ta goyon baya da kulawar da Hon. Rurum ke nunawa ga ‘yan jarida, musamman a cikin watan azumi.
KAROTA Ta Yi Kira Ga Direbobi Da Su Yi Tuki Cikin Hankali A Lokacin Azumin Ramadan
“Wannan tallafi na nuni da yadda Hon. Rurum ke martaba aikin jarida da kuma goyon bayan walwalar ‘yan jarida a wannan lokaci mai albarka,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta jaddada cewa irin wannan tallafi na ƙarfafa dangantaka da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki da kafofin watsa labarai, tare da yin kira ga sauran shugabanni da su yi koyi da hakan
NORP ta yi addu’a ga Hon. Rurum, tana fatan Allah Ya saka masa da alheri da ci gaba da ba shi nasara wajen wakiltar al, ‘umma.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
