News
DA DUMI-DUMI: An Tabbatar Da Ganin Watan Ramadan A Naeriya, Azumi Zai Fara Gobe
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da ganin watan Ramadan a Nigeria.
A wata sanarwa da ya fitar yayin taron manema labarai a fadarsa da ke Sokoto, Sarkin Musulmi ya ce:
Kungiyar Yan Jaridu Ta Yabawa Dan Majalisa Rurum Bisa Tallafawa ‘Ya’yanta A Lokacin Azumin Ramadana
“Mun sami labarin ganin watan Ramadan a yau Juma’a, bayan tantance sahihancin labarin kuma mun amince da batun ganin watan. Don haka, gobe Asabar ce 1 ga watan Ramadan na shekarar 1446 bayan Hijira.”
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa wannan sanarwa na nufin Musulmi a fadin Nigeria za su fara azumin watan Ramadan daga gobe Asabar.
A tun farko, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin a fara duban jinjirin watan Ramadan a yau Juma’a, 29 ga Sha’aban, domin tantance zuwan watan Ramadan.
Allah ya karba ibadunmu, ya sa mu yi azumi lafiya!
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News4 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
