News
AZUMI: Darasi Na Hakika Ga Rayuwar Dan Adam
DAGA HAJARA MAHMUD UMAR
Azumi wata makaranta ce babba da Allah Subahanahu Wata’ala ya wajabta wa dukkanin musulmi mai lafiya da hankali domin tsaftace zuciya da jiki, tare da kusanci ga Ubangiji.
A lokacin azumi, mai azumi na taro wasu rabe-rabe na ibada, kamar yin hakuri da yunwa, kishin ruwa, da kaucewa duk wani abu da zai rage masa lada.
Tsohon Ɗan Wasan Arsenal, Mesut Ozil, Ya Shiga Siyasa a Turkiyya
Hakuri na daga cikin manyan darussan da Ramadan ke koya wa musulmi, domin juriya da jure kowane irin yanayi da ka iya samuwa a rayuwa.
Baya ga haka, azumi na koyar da gaskiya da tsoron Allah, domin mai azumi yana gudanar da ibadarsa ne tsakaninsa da Allah ba tare da kowa yana gani ba.
Hakan na nuni da cewa azumi na kara dankon aminci da ibada tsakanin bawa da Mahaliccinsa.
Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa:
“Ku yi azumi, za ku samu lafiya.”
Wannan na nuni da cewa azumi na da matukar tasiri wajen tsaftace jiki da kwantar da zuciya. Yana kara karfin imani, yana kuma wanke duk wani datti na zunubi.
A kalla idan za a yi azumin watan Ramadan, musulmi na da bukatar garan bawol domin samun lada da lafiyar jiki, kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya karantar. Azumi na zama zakka ga jiki, yana tsaftace shi kuma yana kara kusanci da Allah Subahanahu Wata’ala.
