News
RAMADAN: Sakon Shugaba Tinubu Ga Musulmai.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ina taya ‘yan uwa musulmai ‘yan Najeriya da duniya bakiɗaya a yayin da muke shiga wannan wata na Ramadan.
Muna gode wa Allah maɗaukakin sarki da ya ba mu ikon ganin wannan wata wanda babban bigiri ne na imani a addinin musulunci.
Ina fatan wannan ibada ta azumi da sadaukarwa ya sada mu da samun ingantacciyar lafiya da kyautata imaninmu da yi wa rauwarmu albarka.
Watan Ramadan wata ne na sabunta imaninmu da alaƙarmu tsakaninmu da Allah da ba mu ikon zama masu kyautatawa ga al’umma.
Wannan wata ne na farin ciki da tsantseni da tausayi da naƙasa. Ina kira ga dukkan musulmai da su yi riƙo da tausayi da ƙanƙan da kai da sadaukar da kai da wannan wata ya ƙunsa. Don haka, ya kamata mu yi amfani da wannan dama wajen kyautata alaƙarmu da Allah da kuma ɗaiɗaikun mutane da haɗin kai da rungumar zaman a cikin al’ummarmu.
Wannan azumin wannan shekara na da muhimmanci domin ta zo a daidai lokacin da ake sabunta fatan ‘yan Najeriya.
Gwamnatinmu ta duƙufa wajen kawo tsare-tsare da za su samar da kyakkyawan sakamako kamar yadda ake gani ta fuskar tattalin arziƙi.
Ma’aunin tattalin arziƙi na rubu’in ƙarshen shekarar 2024 ya fito da irin cigaban da aka samu daga shekarar 2023.
Irin tsadar kayan da ake fama da shi a yanzu sun sauko da samar da sauƙin da al’umma suka daɗe suna jira ga ‘yan Najeriya. Haka ma farashin sauya kuɗin ƙasashen waje. Sannan farashin mai yana faɗuwa wanda ke nuna kyakkyawar makomar Najeriya.
A yayin da muke cikin wannan wata, muna fatan samun yabanya mai kyau. Mun shirya inganta samar da abinci da kuma tabbatar da dogaro da kai da wadata ƙasar nan da abinci ta hanyar ba wa manoma tallafi na kayan amfanin gona na zamani da kawo dabaru na noma. Wannan mataki da muka ɗauka zai tabbatar da cigaban ƙasar nan.
A wannan wata mai tsarki, ina kiran ‘yan Najeriya da su haɗa hannu wajen yi wa ƙasarmu addu’a na samun cigaba. Ya kamata mu nemi taimakon da jagorancin da kariyarsa ga ƙasar nan.
Ina yi wa dukkan musulmi fatan gudanar da Azumin watan Ramadana cikin farin ciki da kwanciyar hankali da sabunta imaninmu. Ina addu’ar Allah ya sa mana albarka a wannan wata da samun haske a zuciyoyinmu da gidajenmu da samun tsira a wannan wata.
Fatan za a yi azumin Ramadana lafiya.
