News
Rundunar ‘Yan Sandan Bauchi Ta Kama Wata Mata Bisa Zargin Kashe Kishiyarta
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wata mata mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28, bisa zargin kashe kishiyarta Hajara Isa, mai shekaru 20, a unguwar Kofar Dumi da ke cikin birnin Bauchi.
Binciken farko ya nuna cewa wadda ake zargi ta shake Hajara har ta mutu, sannan ta yi kokarin boye laifinta ta hanyar zuba mata ruwan zafi da kona gawarta da buhun robobi.
Ma’aikatan KSIP Sun Koka Kan Rashin Biyan Su Mafi Karancin Albashi Na N71,000 A Kano
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fara gudanar da bincike na tsanaki domin tabbatar da an gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu.
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa hukuma hadin kai wajen bayar da sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya ajihar.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
