News
Cutar Sankarau Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Akalla 26 A Jihar Kebbi
Cutar sankarau ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 26 a jihar kebbi, inda gwamnatinta ta tabbatar da cewa wannan lamari na bullar cutar yana iya karuwa cikin mako guda.
Kwamishinan lafiya na jihar, Alhaji Musa Ismaila, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Talata.
Babbar Motar Dakon Yashi Ta Hadasa Hadarin Da Ya Haifar Da Mutuwar 3, Jikkata 3 A Kano
Ismaila ya bayyana cewa cikin mako bakwai, an samu karin yaduwar cutar a kananan hukumomi na Gwandu, Jega, Aliero da Argungu.
A cewarsa, mutane 248 ne ake zargi da dauke da alamu na cutar kamar zazzabi, matsanancin ciwon kai, ciwon ciki, amai, gudawa .
“Daga cikin samfurin da aka tura zuwa dakin gwaje-gwaje na National Reference Laboratory na Abuja, sakamakon guda biyu sun tabbatar da cutar a cikin kananan hukumomi na Gwandu da Jega,” in ji kwamishinan.
A cewar Ismaila, an dauki matakan gaggawa ciki har da tallafin magunguna da kayan agaji na Naira miliyan 30, wanda aka raba wa kananan hukumomin da suka shafa.
Har ila yau, cibiyoyin kiwon lafiya na musamman sun kafa a wuraren da lamarin ya fi tsanani.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani mutum da ke da alamun cutar zuwa cibiyar lafiya mafi kusa domin daukar matakin daya dace.
