Connect with us

News

CP Bakori Ya Karɓi Ragamar A Matsayin Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Kano

Published

on

CP Bakori 1 (1)

 

Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya karɓi ragamar shugabanci a matsayin Kwamishina na 47 a hedikwatar ‘yan sanda ta Kano.

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana a wata sanarwa ranar Litinin cewa CP Bakori ya gaji tsohon kwamishinan da aka ɗaga mukaminsa zuwa Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda (AIG).

CP Bakori, gogaggen ɗan sanda ne da ke da ƙwarewar fiye da shekaru 28. An haife shi a ranar 6 ga Fabrairu, 1969 a ƙaramar hukumar Katsina ta Jihar Katsina. Ya shiga aikin ‘yan sanda a ranar 15 ga Agusta, 1996 a matsayin Cadet ASP, inda ya sami horo a Kwalejin ‘Yan Sanda ta Wudil, Kano.

Advertisement

Teloli: Sako Na Musamman Ga ‘Yan Uwa Abokan Aiki – B. Imam Bespoke Tailoring

Ya mallaki digirin digirgir (PhD) a fannin Nazarin Zaman Lafiya da Rikici daga Jami’ar Jihar Nasarawa, da kuma digiri na biyu a fannin Tsare-Tsare da Zaman Lafiya daga Jami’ar Kaduna, tare da digiri na biyu a fannin Gudanarwa daga Jami’ar Abuja.

CP Bakori ya halarci manyan kwasa-kwasai da dama a fannin aikin ‘yan sanda, ciki har da horon aiki na Rundunar ‘Yan Sandan Mobal (PMF), Kwasa-kwasan Bincike na Musamman, da Horon Jagoranci da Kwamandoji.

Advertisement

Har ila yau, ya yi tafiya zuwa ƙasashe fiye da 25 a Afirka, Asiya da Turai, inda ya ƙara samun fahimta kan dabarun aikin ‘yan sanda na duniya.

A lokacin da yake aiki, CP Bakori ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da O/C Patrol da Guard a Akwanga, DPO a Lafia da Doma, ADC ga Kakakin Majalisar Wakilai, Kwamandan ‘Yan Sanda na 24 PMF da ke kula da tsaron Fadar Shugaban Ƙasa, da Kwamanda a Rundunar 17 PMF, Akure.

Advertisement

Sauran mukaman da ya riƙe sun haɗa da Shugaban Sashen CID a Jihar Ribas da Bayelsa, Kwamandan JTF a Bayelsa (Operation Doo Akpo), da Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da sashen Homicide a Hedikwatar CID, Abuja.

Da yake karɓar mulki, CP Bakori ya sha alwashin yin aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Kano. Ya kuma yi kira ga al’umma da su ba da haɗin kai tare da samar da bayanai masu amfani domin yaƙi da aikata laifuka.

Advertisement

Rundunar ‘Yan Sanda ta Kano ta bukaci jama’a da su ba sabon kwamishinan goyon baya domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending