Connect with us

News

Teloli: Sako Na Musamman Ga ‘Yan Uwa Abokan Aiki – B. Imam Bespoke Tailoring

Published

on

images

 

A yayin da watan Ramadan ke tafiya, ana fuskantar matsala daga wasu ‘yan uwarmu teloli da ke fakewa da aikin yau da kullum wajen kin tashi yin sallah akan lokaci. Wannan hali na iya jawo gurbacewar ibada da kuma rashi amfani da wannan wata mai albarka.

Advertisement

Haka zalika, tsayuwar dare da karatun littafin Allah (SWT) – wanda yake daga cikin manyan ayyukan ibada a Ramadan – yana yawaita samun sakaci daga wasu teloli, wanda ke barin su a baya wajen samun albarkar watan.

Shiru-shirun Fubara Ba Tsoro Ba Ne – Sakataren Gwamnatin Rivers

Shugaban kamfanin B. Imam Bespoke Tailoring yana mai tunatar da ‘yan uwa teloli muhimmancin biyayya ga Allah (SWT), musamman a wannan wata na rahama da falala. Aiki yana da muhimmanci, amma bai kamata ya hana mu sauke farali da ibada ba.

Advertisement

A ƙarshe, ya jaddada cewa teloli su kasance masu cika alkawari da kuma riƙon amana wajen sauke nauyin da suka ɗauka ga abokan hulda. Wannan zai kara musu daraja da albarka a harkokin kasuwancinsu da rayuwarsu gaba ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending