Connect with us

News

Shiru-shirun Fubara Ba Tsoro Ba Ne – Sakataren Gwamnatin Rivers

Published

on

Siminalaye Fubara 750x430

 

Sakataren gwamnatin jihar Rivers, Tammy Danagogo, ya bayyana cewa shiru da sanyi-sanyin da Gwamna Siminalayi Fubara ke yi ba alamar tsoro ba ne, illa nuna kishin zaman lafiya da cigaban jihar.

Advertisement

Danagogo ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da Ministan Abuja, Nyesom Wike, da magoya bayansa ke zargin Fubara da ruruta rikicin siyasar jihar.

Kotu Ta Daure Matashi Saboda Ji Wa Makwabcinsa Rauni Da Almakashi A Kano

A cewarsa, Gwamna Fubara mutum ne mai son zaman lafiya, wanda ya fi mayar da hankali kan ci gaban al’ummar Rivers fiye da shiga rigingimu. Ya kara da cewa hakan ne yasa yake kaucewa duk wata rigima da ka iya kawo cikas ga ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

Advertisement

Danagogo, wanda ya taɓa zama sakataren gwamnati a wa’adin mulkin Wike, ya ce burin Fubara shi ne tabbatar da dimokuraɗiyya mai amfani ga al’ummar jihar.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending