News
Ya Kamata A Inganta Tsaro Da Samar Da Wutar Lantarki A Arewa Tare Da Bunkasa Harkokin Noma Da Kiwo —Comr. Abba Alra-iwas
Shahararren mai fafutuka, Comr. Abba Alra-iwas, ya bayyana bukatar yin garambawul ga yankin Arewa, yana mai jaddada cewa idan har ana matukar kaunar yankin, to ya zama dole a kara inganta tsaro, a samar da tsayayyar wutar lantarki, tare da bunkasa harkokin noma da kiwo.
Ya yi wannan kira ne ga iyayen kasa, musamman masu rike da madafun iko, da su tashi tsaye domin ceto Arewa daga matsalolin da suka dabaibayeta.
CP Bakori Ya Karɓi Ragamar A Matsayin Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Kano
“Arewa na bukatar kulawa ta musamman. Idan har muna fatan cigaba, dole ne a fuskanci wadannan matsaloli da gaske,” in ji shi.
Ya kara da cewa, matakin farko shi ne tabbatar da tsaro a jihohin Arewa domin rayuwa da kasuwanci su ci gaba yadda ya kamata. Haka nan, samar da wutar lantarki mai inganci zai taimaka wajen bunkasa masana’antu da harkokin kasuwanci.
Baya ga haka, ya jaddada cewa, noma da kiwo su ne ginshikin tattalin arzikin yankin, don haka ya zama dole a samar da ingantattun tsare-tsare domin habaka wadannan bangarori.
Jama’a da dama sun goyi bayan wannan kira, suna mai fatan cewa shugabanni za su dauki matakan da suka dace domin amfanin daukacin al’umma.
