Connect with us

News

Tsoffin Daliban Makarantar CAS Ta Kano Sun Tallafawa Marayun Abokan Karatunsu Da Naira Miliyan 2.8

Published

on

IMG 20250324 WA0029

A wani yunƙuri na taimakon marayu da jin-ƙai, tsoffin ɗaliban makarantar share fagen shiga jami’a (CAS) ta Kano, ajin 2002, sun raba tallafin Naira miliyan 2,780,000 ga ƴaƴan abokan karatunsu da suka riga mu gidan gaskiya.

An gudanar da rabon tallafin ga marayu 73 a harabar makarantar a ranar Lahadi, inda lamarin ya haifar da motsin zuciya ga mahalarta taron.

Advertisement

Hukumar Shari’ah Da Kungiyar WAMY Sun Shirya Shan Ruwa Na Musamman Ga Wadanda Suka Musulunta A Kano

Shugaban kwamitin walwala na ƙungiyar, Mansur Tukur Hotoro, ya bayyana cewa ƴan ƙungiyar sun tara Naira miliyan 2.6 cikin wata guda, sannan suka ƙara Naira dubu 180 daga asusun ƙungiyar don cike gibin da ya rage.

A cewarsa, an raba Naira dubu 50 ga marayun da iyayensu su ka mutu ɗai-ɗai, yayin da masu iyaye biyu su ka samu Naira dubu 40 kowanne, sai masu uku kuwa an bai wa kowannensu Naira dubu 35.

Advertisement

“Mun fara wannan tallafi tun a shekarar 2024 don tunawa da iyalan abokan karatunmu da suka bar duniya. Mun kuduri aniyar ci gaba da wannan aiki har bayan rayuwarmu,” in ji Hotoro.

Ya kuma yi kira ga iyayen da aka barwa marayun da su kula da su yadda Addinin Musulunci ya koyar, tare da yin addu’ar Allah ya gafartawa mamatan.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending