News
Masu Kiwon Kaji Sun Koka Kan Raguwar Ciniki Yayin da Sallah Ke Karatowa
Yayin da bukukuwan Sallah ke karatowa, masu kiwon kaji a jihar Kano da kewaye sun koka kan raguwar ciniki, lamarin da ke barazana ga kasuwancinsu.
A cewar masu kiwon kaji, a baya irin wannan lokaci na Sallah na kasancewa lokacin da ake samun gagarumin ciniki. Sai dai a bana, suna fuskantar kalubale da suka hada da tsadar abincin su, matsanancin zafi da ke kashe kajin, da kuma karancin masu saye.
Mallam Shuaibu Ismail, wani gogaggen mai sayar da kaji, ya bayyana cewa: “A shekarun baya, zuwa wannan lokaci, mun riga mun sayar da mafi yawan kayayyakinmu. Amma bana, saye ya ragu sosai, kuma muna cikin damuwa.”
Haka nan, Jamila Sulaiman, wata mai kiwon kajin broiler, ta ce: “Duk shekara muna shirin wannan lokaci, amma bana mutane ba sa siyan kaji kamar da. Tsadar rayuwa da hauhawar farashin abinci na daga cikin matsalolin da suka shafi kasuwancinmu.”kamar yanda Jaridar DAILY REALITY ta ruwaito
Duk da haka, masu kiwon kajin na fatan cewa yayin da Sallah ke kara matsowa, ciniki zai habaka. Isuhu Wada, wani mai kiwon kaji, ya yi kira ga jama’a da su tallafa musu ta hanyar siyan kajin gida, domin ci gaba da raya al’adun Sallah da bunkasa kasuwancin su.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
