News
INEC Ta Amince da Kiranyen Sanata Natasha Bayan Cikar Ka’idoji
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti, cewa al’ummar mazabar-ta sun cika ka’idojin da ake bukata don yin mata kiranye.
A baya, INEC ta ki karbar korafin da ke neman kiranyen sanatar, bisa dalilin cewa takardar kiranyen ba ta cika ka’idojin da suka hada da bayar da cikakkun adireshi da lambobin wayar wadanda suka sanya hannu ba.
Masu Kiwon Kaji Sun Koka Kan Raguwar Ciniki Yayin da Sallah Ke Karatowa
Sai dai a yau, hukumar ta INEC ta aikawa Sanata Natasha wasika, inda ta tabbatar da cewa al’ummar mazabar-ta sun cike gibin da aka samu, lamarin da ke nuni da cewa ana iya ci gaba da matakan kiranye a kanta.
Advertisements
