News
SATAR KAYAN MAKARANTU: Hukumar NSCDC Ta Kama Mutane Biyar A Kano
Hukumar Kare Rayuka da Dukiyoyin Al’umma ta Kasa (NSCDC), reshen jihar Kano, ta tabbatar da kama wasu matasa biyar da ake zargi da aikata laifin lalata da satar kayayyakin makarantu a cikin birnin Kano.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar, an cafke hudu daga cikin wadanda ake zargi a unguwannin Unguwar Rimi da Unguwa Uku.
Wadanda aka kama sun hada da Abdulbasi Usman (19), Yahaya Isah (20), Abubakar Saddiq Abdullahi (20), mazauna Unguwar Rimi a Kumbotso, da Adamu Murtala (20), mazaunin Unguwa Uku a Tarauni.
Yan Bindiga Sun Mamaye Garuruwa Fiye Da 60 a Filato – Inji Gwamna Muftwang
Ana zargin matasan da laifin lalata da kuma satar kayayyakin makarantu mallakin gwamnatin jihar Kano, ciki har da makarantar sakandare ta Unguwar Rimi da ta Unguwa Uku.
Kayayyakin da suka hada da kwanon rufi, rodika, bokitai, kujeru guda 203, tabarma, tagogi guda bakwai, fankoki biyu da sauran kayayyakin koyarwa da na amfani na yau da kullum ne ake zargin an sace.
Haka zalika, an kama mutum na biyar mai suna Alasan Inusa, dan shekara 17, mazaunin Gidan Tela PRP a karamar hukumar Dambatta, bisa zargin satar fala-falan lantarki da wasu kayan lantarki a yankin.
Jami’in ya ce bincike ya kammala kan wadanda ake zargi, kuma tuni shirye-shirye sun yi nisa wajen gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
Hukumar NSCDC ta jaddada kudurinta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, karkashin jagorancin kwamandan jihar Kano, Shafi’u Abdulmumini, inda ta bukaci hadin kan jama’a wajen bayar da rahoton duk wani aiki na laifi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
