Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Mamaye Garuruwa Fiye Da 60 a Filato – Inji Gwamna Muftwang

Published

on

FB IMG 1744241705536

Gwamnan Jihar Filato, Mista Caleb Muftwang, ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke kara kazancewa a wasu sassan jihar, inda ya ce a halin yanzu ‘yan bindiga sun mamaye akalla garuruwa 64 a fadin jihar.

Muftwang ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Talata. A cewarsa, lamarin ya zama abin takaici, duba da yadda al’umma ke ci gaba da fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda da ke samun goyon baya daga wasu da ba a san ko su wanene ba.

Advertisement

Cutar Sankarau Ta Yi Ajalin Mutane 151 A Najeriya – NCDC

“Abin da ya fi muhimmanci a halin yanzu shi ne hukumomin tsaro su mai da hankali wajen gano masu daukar nauyin wadannan hare-hare,” in ji Gwamnan.

Ya bayyana cewa, wasu daga cikin garuruwan da aka kai wa hare-hare a shekarar 2023 na daga cikin yankunan da ‘yan ta’adda ke ci gaba da mamaya, inda mazauna yankunan suka koma domin ci gaba da rayuwa duk da hadurran da ke tattare da hakan.

Advertisement

Gwamnan ya bayar da misali da kauyen Ruwi, inda aka kai hari a bara wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 17. Duk da haka, mazauna kauyen sun sake komawa sun gina gidajensu.

Ya kara da cewa, tun kusan shekaru goma ke nan da ake fama da wadannan hare-hare, abin da ke nuna cewa akwai wata babbar makarkashiya da ke bayan lamarin.

Advertisement

Muftwang ya bayyana cewa mafi yawan garuruwan da ‘yan bindigar suka mamaye na cikin kananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi da Riyom, inda ma har sun sauya wa garuruwan suna bayan sun karbe su.

A karshe, Gwamnan ya yi fatan cewa nan ba da jimawa ba, hukumomin tsaro za su hada kai don kawo karshen wannan matsala da ta addabi jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending