Connect with us

News

Cutar Sankarau Ta Yi Ajalin Mutane 151 A Najeriya – NCDC

Published

on

NCDC

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta bayyana damuwa kan yadda cutar sankarau ke ci gaba da karfi a sassan Najeriya, inda cutar ta yi sanadin mutuwar mutane 151 tun daga watan Oktoba 2024 zuwa yanzu.

Cutar dai ta fi kamari a yankunan arewacin kasar, inda galibin wadanda annobar ta fi shafa su ne kananan yara da ke zaune a karkara. A cewar NCDC, cutar ta yadu zuwa jihohi 23 daga cikin 36 da ke kasar, lamarin da ke kara tayar da hankalin hukumomin lafiya.

Advertisement

Real Madrid Ta Sha Kashi A Hannun Arsenal Da Ci 3 Babu Ko Daya

Mai magana da yawun NCDC, Sani Datti, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa karancin tallafin da ake samu daga kasashen waje, musamman na Amurka, ya kara tsananta halin da ake ciki. Ya ce dakatar da tallafin da ke shigo wa kan harkokin lafiya na daga cikin manyan kalubale da kasar ke fuskanta a yaki da wannan annoba.

Sai dai Datti ya ce Najeriya ta samu karin tallafi daga cibiyar samar da rigakafi ta duniya, Gavi, inda aka tura kimanin allurar rigakafi miliyan guda domin taimaka wa wajen dakile yaduwar cutar. Ya kara da cewa annobar sankarau na da nasaba da sauyin yanayi, musamman tsananin zafi da ake fuskanta a arewacin Najeriya.

Advertisement

Hukumar NCDC na ci gaba da daukar matakai tare da hadin gwiwar jihohi da kungiyoyi na cikin gida da na waje, domin dakile yaduwar cutar da kuma ceto rayukan al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending