News
Yadda Aka Buɗe Makarantar Koyon Wanki Da Guga A Asibitin AKTH
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya kafa makaranta ta musamman da ke koyar da yadda ake wanki da gugar kayan asibiti — ita ce irinta ta farko a Najeriya.
Makarantar dai na koyar da fasahar tsaftace barguna, zannuwan gadon asibiti, da kayan tiyata na likitoci da ma’aikatan jinya, inda ɗaliban ke samun horo mai zurfi a fannin.
An Kama Wasu Jami’an Tsaro Huɗu Da Ake Zargi Da Taimakawa Ayyukan Ta’addanci
Tuni ɗaliban farko sun fara samun Difloma ta Ƙasa (ND), kuma akwai shirin fara Babbar Difloma (HND) domin ci gaba da ƙwarewa.
Hukumar kula da manyan makarantu na fasaha (NBTE) ta amince da tsarin karatun makarantar na tsawon shekaru biyar, domin ci gaba da horas da sabbin ɗalibai.
A cewar shugaban makarantar, Mohammed Kabir Ahmad, makarantar da aka fara domin ma’aikatan AKTH yanzu tana karɓar ɗalibai daga faɗin ƙasar nan ta hanyar JAMB, har mutum 60 a kowace shekara.
Ya ce akwai matasa da dama da cibiyoyin lafiya na gwamnati da hukumomin jihohi da tarayya ke ɗaukar nauyin karatunsu, yayin da wasu ke karatu da kansu domin su samu sana’a a fannin tsaftace kayan asibiti da na masana’antu.
Shugaban ya ƙara da cewa wani tsohon gwamna ya ɗauki nauyin matasa 150 su yi karatu a makarantar, kuma kowanne daga cikinsu ya samu injin wanki guda biyu bayan kammala karatunsu domin su kafa sana’arsu.
Wannan makaranta na daga cikin sabbin hanyoyin da ake bi domin inganta tsaftar asibitoci da kuma ƙarfafa sana’o’in hannu ga matasa.
