News
Kyari Ya Ce Ba Ya Hannun EFCC
Tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Engr. Mele Kyari, ya ce ba gaskiya ba ne rade-radin da ke yawo cewa Hukumar EFCC ta kama shi ko tana tsare da shi.
Kyari ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a daren Asabar, 3 ga watan Mayu, yana mai cewa yana rayuwa cikin gaskiya da tsoron Allah tun lokacin da ya fara aiki a NNPC fiye da shekaru 30 da suka wuce.
Yadda Aka Buɗe Makarantar Koyon Wanki Da Guga A Asibitin AKTH
“Ban yi wa Najeriya kadai aiki ba, na yi da tsoron Allah,” in ji shi cikin martaninsa ga rade-radin da ke yawo.
A baya dai rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC ta fara binciken wasu tsofaffin jami’an NNPCL, musamman wadanda suka rike mukamai a matakin gudanarwa da kuma matatun man Warri, Kaduna da Fatakwal.
Wata jaridar yanar gizo ce ta wallafa cewa an kama Kyari don amsa tambayoyi kan zarge-zargen almundahana, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.
Sai dai Kyari ya yi fatali da ikirarin, yana mai cewa ba ya cikin tsare, kuma bai da hannu a cikin duk wata almundahana da ake zargi da ita.
A kwanakin baya ne aka fara duba wasu kudade da suka hada da Dala biliyan 2.96 da ake zargin an karkatar, inda aka ruwaito cewa an gano Naira biliyan 80 a asusun wani tsohon darekta a kamfanin.
