Connect with us

News

India Ta Hana Shigo Da Kaya Daga Pakistan

Published

on

images (7)

India ta hana shigo da duk wani kaya da ake samarwa ko shigowa da su daga Pakistan, a wani sabon mataki da ke nuna yadda dangantakar kasashen biyu ke kara tsananta.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Kasuwanci ta Ƙasashen Waje a India ta fitar ta ce matakin ya fara aiki nan take.

Advertisement

Kyari Ya Ce Ba Ya Hannun EFCC

India ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan harin da ya kashe mutane 26 da ke yawon bude ido a yankin Pahalgam na Kashmir, inda ta zargi Pakistan da hannu a harin.

Sai dai Pakistan ta musanta zargin, tana mai cewa tana da bayanai na sirri da ke nuna cewa India ce ke shirin kai mata hari.

Advertisement

A matsayin martani, Pakistan ita ma ta dakatar da huldar kasuwanci da India, ta kori wasu jami’an diflomasiyya daga New Delhi, tare da hana jiragen saman Indiya shiga kasar.

Bayan hakan, India ta ce ba za ta ƙara bari jiragen ruwa daga Pakistan su shiga cikin kasar ba, haka zalika nata jiragen ba za su ratsa cikin Pakistan ba.

Advertisement

Wannan sabani na baya-bayan nan ya biyo bayan dadadden rikici ne dangane da yankin Kashmir, wanda kasashen biyu ke ikirarin mallaka, kuma ke zama tushen rikici a tsakaninsu.

Yanzu haka, zaman dar-dar tsakanin kasashen biyu ya janyo raguwa wajen yawon bude ido a Kashmir, inda mutane ke fargabar afkuwar wani sabon hari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending