Connect with us

News

Kwankwaso Da Ganduje Su Ne Matsalar Da Ke Hana Jihar Kano Ci Gaba – Cewar Sheikh Ibrahim Khalil

Published

on

images

Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa manyan ’yan siyasa biyu — Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje — su ne matsalar da ke hana jihar Kano ci gaba.

Sheikh Khalil ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na DAN UWA RANO, inda ya ce rikici da gaba-gaba tsakanin wadannan shugabanni biyu ne ya janyo rabuwar kai a tsakanin malamai da kuma al’ummar jihar gaba ɗaya.

Advertisement

Wani Matashi Ya Rasa Ransa Saboda Ya Ziyarci Budurwarsa A Kano

“Wasu malamai sun kama tafarkin Kwankwaso, wasu kuma sun kama na Ganduje. Wannan rabe-raben ya hana zaman lafiya da cigaban jihar,” in ji Sheikh Khalil.

Da aka tambaye shi a tsakanin Kwankwaso da Ganduje wanda ya fi cancanta a bi, sai Sheikh Khalil ya ce:“Gaskiya, ba ɗayansu da ya cancanci a bi.”

Advertisement

Sheikh Ibrahim Khalil shi ne shugaban Majalisar Malaman Kano, kuma ya tsaya takarar gwamnan jihar Kano a 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Jawabinsa ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da majalisun jama’a, inda wasu ke ganin cewa rikicin siyasa tsakanin Kwankwaso da Ganduje na hana Kano kwanciyar hankali da ci gaba.

Advertisement

A halin yanzu dai, mutane da dama na tambayar yadda makomar siyasar Kano za ta kasance a zaben 2027 mai zuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending