Connect with us

News

Yadda Jirgin Soji Ya Kashe ’Yan Sa-kai 20 A Zamfara Bisa Kuskure

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Aƙalla mutane 20 da ake zargin ’yan sa-kai ne sun rasa rayukansu, sakamakon wani harin sama da jiragen yakin dakarun sojin saman Najeriya (NAF) suka kai a ƙauyen Mani da ke Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa jiragen sojin sun kai harin ne da nufin fatattakar ’yan bindiga da suka kai farmaki kan manoma a rana tsaka, inda suka sace sama da mutum 50. Sai dai, bisa kuskure, harin ya rutsa da ’yan sa-kai da ke kokarin taimakawa wajen kare al’umma daga harin.

Advertisement

Jami’ar Northwest Ta Ƙara Kuɗin Makaranta Duk da Ragen Kashi 50% Da Gwamnatin Kano Ta Yi

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa, “Mun kira jami’an tsaro bayan harin ’yan bindiga, amma abin mamaki sai muka ga jirgin soji ya iso ya fara harbin ’yan sa-kai.”

Ya ci gaba da cewa, “’Yan bindiga sun tafi da mutane 50, kuma yayin da muke ƙoƙarin ceto sauran mutanenmu, sai muka ga jirgin soji ya fara harbin mu. Dole kowa ya nemi mafaka, wasu ma sai da suka kwanta ƙasa kamar matattu domin tsira.”

Advertisement

Wani mazaunin garin ya bukaci hukumomin tsaro da su ƙara kaimi da kuma taka-tsantsan wajen gudanar da ayyukansu, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.

Kawo yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.

Advertisement

Harin na Zamfara ba shi ne na farko da jiragen soji ke kai wa fararen hula ko ’yan sa-kai bisa kuskure ba. A watan Janairun 2025, jirgin sojin saman Najeriya ya hallaka mutane 16 a ƙauyen Tungar Kara, ciki har da manoma da ’yan sa-kai, bayan an zarge su da zama ’yan bindiga.

Haka zalika, a watan Disambar 2024, wani harin sama da aka kai a Jihar Sakkwato ya yi sanadin mutuwar fararen hula 10, wanda Gwamnan jihar ya bayyana a matsayin harin kuskure.

Advertisement

A watan Disamba na shekarar 2023 kuma, fiye da mutane 100 sun mutu a wani harin sama da aka kai a yayin taron Mauludi a Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, wanda shi ma aka ce an kai shi ne bisa kuskure.

Ana ci gaba da kiraye-kirayen da ake yi ga gwamnati da hukumomin tsaro da su duba hanyoyin da za a kauce wa irin waɗannan hare-haren kuskure, musamman a yankunan da ke fama da rikicin ’yan bindiga.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending