News
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Karyata Jita-Jitar Sace Mutane 200 A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta musanta wani rahoto da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa an yi garkuwa da mutane sama da 200 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Kaduna, yana mai cewa labarin ƙarya ne tsagwaronta, kuma ba shi da wani tushe na gaskiya.
Tsohon Ministan Ilimi Farfesa Jibril Aminu, Ya Rasu Yana Da Shekaru 85 A Duniya.
A cewarsa, cikin shekaru biyu da suka wuce, babu wani rahoton sace mutane da aka samu a kan hanyar, yana mai jaddada cewa rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro na gudanar da sintiri da sa ido a kai a kai don tabbatar da tsaron rayukan jama’a da lafiyar hanya.
“Hanyar Abuja zuwa Kaduna tana karkashin tsauraran matakan tsaro, kuma har yanzu ba mu da wani rahoton garkuwa da mutane a nan cikin shekaru biyu da suka wuce,” in ji DSP Hassan.
Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yi kakkausar gargadi ga masu yada labaran ƙarya da kafafen yada labarai da ke bazawa ba tare da tantance gaskiya ba, yana mai cewa hakan na iya jefa al’umma cikin fargaba da tashin hankali.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.
