News
Gwamnatin Kano Ta Taya Sabon Shugaban Hima FM Alh Isma’il Yusuf Makwarari Munar Kama Aiki
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa kafa tashar Himma Radio da TV, wadda ta mayar da hankali kan shirye-shiryen da suka shafi harkokin noma da kiwo, na daga cikin muhimman matakan da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar da habaka rayuwar al’umma.
Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai na jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, domin taya sabon Shugaban tashar Himma FM, Alhaji Isma’il Yusuf Makwarari, murna da nadin da aka yi masa.
A cewarsa, gwamnatin Kano ta gamsu da yadda aka ɗora kwarya a gurbinta, ganin yadda sabon shugaban tashar ke da gogewa da jajircewa, musamman duba da irin ƙwarewarsa a fagen aikin jarida da sha’awarsa ga ci gaban jihar Kano.
Kwamishina Waiya ya nuna fatan cewa Makwarari zai taka rawar gani wajen fito da shirye-shiryen da za su habaka harkokin noma da kiwo, tare da lalubo sabbin dabaru da za su taimaka wa manoma da makiyaya a fadin jihar.
Ya bukaci manoma, makiyaya da daliban fannin noma da su rungumi tashar Himma FM domin amfana da shirye-shiryen ilimantarwa da wayar da kai da tashar ke yadawa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta sana’o’insu da rayuwarsu gaba ɗaya.
A karshe, Waiya ya yi kira ga ‘yan kasuwa da kamfanoni da su rika tallata hajarsu ta hanyar tashar, domin samun kudaden shiga da za su taimaka mata ta tafiyar da ayyukanta cikin nasara. Haka kuma ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da bai wa Himma FM cikakken goyon baya domin cimma manufofinta na bunkasa tattalin arzikin jihar ta hanyar harkokin noma da kiwo.
