News
Yan ta’adda sun kashe mutane 5 tare da sace wasu 17 A Cikin Sabbin Hare-hare A Jihar Kaduna
Daga kabiru basiru fulatan
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kashe mutum biyar da suka hada da malami daya da wani dattijo mai shekaru 70 a cikin kauyuka uku na Dogo Dawa, Layin Mahuta da Tabanni a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar ta Birnin-Gwari Vanguards for Security and Good Governance, Ibrahim Abubakar Nagwari, ya ce a yayin hare-haren na daban, wanda ya faru tsakanin ranar Litinin zuwa Juma’a, ‘yan ta’addan sun kuma sace mutane 17.
Nagwari ya kuma bayyana cewa mutane 32 daga cikin 46 da suka dauke bayan sun kai hari a Ungwan Bula da Ijinga makonni uku da suka gabata ‘yan bindigar sun sako su bayan sun biya kudin fansa N16m da suka nema.
Ya kara da cewa, a ranar 14 ga watan Maris, ‘yan ta’addan sun kai hari a kan hanyar Dogo Dawa zuwa Zariya a Gabashin Birnin-Gwari, inda aka kashe Haruna Tanko Dogo Dawa tare da yin garkuwa da wasu mutane takwas.
Nagwari ya ci gaba da cewa, a tsakanin Laraba da Alhamis, an kashe wani Alhaji Abdullahi Abubakar, malamin makaranta tare da Layin Lasa-Tabanni, yayin da aka kashe wani tsoho mai shekaru 70, sannan “an sace mata a Layin Mahuta Tabanni,.‘yan fashi sun yi awon gaba da su
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
-
News3 days ago
Uba Ya Nemi Kotu Ta Tilasta Wa ’Yarsa Ta Fitar Da Mijin Aure A Kaduna
