Connect with us

News

Tsadar Taki Ya Sa Manoma Sun Daina Noman Dawa Da Masara

Published

on

Tsadar takin zamani da magungunan feshi ta sa manoma da dama a jihar Kaduna sun daina noman masara da dawa a daminar bana, inda suka karkata ga noman kayan lambu da kayan miya da suka fi saukin nomawa da kuma samun riba.

Wani hasashen masana ya nuna cewa za a iya fuskantar matsalar karancin hatsi a bana, sakamakon yadda manoma ke barin noman masara da dawa, suna komawa noman tumatir, araragu, tattasai da barkono.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Ƙara Kuɗin Wutar Lantarki 

Tsohon shugaban Hukumar Gudanar da Bincike kan Harkokin Noma na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Farfesa Faguji Ishyaku ne ya bayyana hakan a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Zariya ranar Talata.

Farfesa Ishyaku ya ce manoma sun san irin tsadar da takin zamani da magungunan feshi suka yi a bana, shi ya sa suka bar noman hatsi da yawansu suka koma ga kayan lambu da wake.

Advertisement

“Manoma sun fi karkata ga noman kayan miya da kayan lambu saboda suna ganin riba za su samu. Amma wannan sauyi yana da illa matuƙa ga sha’anin abinci a ƙasar nan,” in ji shi.

Ya ce idan aka ci gaba da wannan yanayi, Najeriya za ta ci gaba da dogaro da abincin waje, wanda zai ƙara dagula halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Advertisement

Shi ma wani manomi da ke Zariya, Ahmed Abubakar, ya tabbatar da haka, inda ya ce yawancin manoma sun daina noman masara, dawa da shinkafa, sun koma noma barkono, kubewa da albasa.

Ya ce wannan sauyi na da nasaba da hauhawar farashin taki da kuma yadda ake ci gaba da shigo da hatsi daga kasashen waje cikin ƙasa.

Advertisement

“Yanzu haka buhun masara mai nauyin kilo 100 yana kai wa tsakanin Naira 38,000 zuwa Naira 45,000. Amma buhu ɗaya na takin GDAP mai nauyin kilo 50 yana kai Naira 75,000,” in ji shi.

“Wato ba buhu ɗaya na masara ko dawa ne zai iya siyan buhun taki ba. Amma idan ka noma barkono ko wake, za ka iya siyan taki, har ka rage,” a cewarsa.

Advertisement

Ya ce wannan sauyin yana iya kawo cikas ga kokarin gwamnati na tabbatar da wadataccen abinci a cikin gida.

A cewarsa, Najeriya na bukatar tan miliyan takwas (8) na masara a shekara domin cika bukatar jama’a, amma tana iya samar da tan miliyan shida da rabi (6.5) ne kacal.

Advertisement

Ya kara da cewa jihar Kaduna na daga cikin jihohin da suka fi karfin noman masara a Najeriya, amma da yadda manoma ke juya baya ga noman hatsi, akwai yiyuwar komai zai sauya a jihar da ma kasa baki daya.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending