News
Hukumar Kula da Yansanda ta gurfanar da manyan jami’ai fiye da DUB 150 bisa zargin take hakkin fararen hula
Hukumar Kula da Ƴansanda a Najeriya ta gurfanar da manyan jami’an Ƴansanda sama da 150 a gaban kwamitin ladabtarwa, bisa zargin aikata abubuwan da suka sabawa dokokin aiki.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an da aka gurfanar sun fuskanci tuhume-tuhume da suka shafi wulakanta aikin Ƴansanda da kuma take hakkin fararen hula, musamman a lokutan gudanar da ayyukansu a wuraren aiki.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗi Kan Yiwuwar Ambaliya A Kano Da Sauran Jihohi 10
Wannan mataki na daga cikin kokarin hukumar wajen gyara fannin Ƴansanda da kuma dawowa da amincewa tsakanin jami’an tsaro da al’umma
Advertisements
