Connect with us

News

Ƴan Sanda Sun Kama Shugaban Ƴan Ta’adda Da Ya Addabi Kaduna Da Katsina

Published

on

Suspects with stolen Toyota Prado SUV and two motorcycles 750x430

Rundunar ƴan sanda a jihar Kaduna ta ce ta cafke wani shugaban ƴan bindiga da ake nema ruwa a jallo tsawon shekaru 11, a wani samame da ta kai a unguwar Galadima da ke yankin Shika, a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar.

Ana zargin mutumin, mai suna Mati Bagio, da jagorantar wata ƙungiyar yan ta’adda da ke kai hare-hare a sassan jihar Kaduna da Katsina.

Advertisement

ICPC Zata Gurfanar Da Shugaban KANSIEC A Gaban Kotu

A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an kama Bagio ne da safiyar Juma’a, 18 ga Yuli 2025, bisa bayanan sirri da aka samu.

“Jami’an sashin yaƙi da garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin CSP Sani Zuntu ne suka kama shi a gidansa, inda aka gano bindigu da dama da alburusai,” in ji SP Hassan.

Advertisement

Abubuwan da ƴan sanda suka ce sun kwato sun haɗa da Bindiga kirar AK-47 guda biyu (ɗaya daga ciki an sarrafa shi a gida), Bindiga pump-action guda ɗaya, Pistols guda biyu, Majinyar bindigu guda shida, Alburusai fiye da 100, Wuka, fitilun hannu guda biyu, da sanda na buɗe bindiga

SP Hassan ya ce an dade ana nemansa saboda rawar da ya taka a hare-haren da suka faru a Giwa, Hunkuyi, Faskari, Dandume da Funtuwa – dukkansu a jihohin Kaduna da Katsina.

Advertisement

Yanzu haka yana tsare a hannun ƴan sanda yayin da ake ci gaba da bincike, tare da ƙoƙarin kamo sauran mambobin ƙungiyar sa.

An kwato motar da aka sace a Abuja

Advertisement

A wani samame daban, rundunar ƴan sanda ta ce ta gano wata motar kirar Toyota Prado da aka sace a Abuja, kuma aka gano ta a Kaduna a ranar 17 ga Yuli.

“Motar da aka sace a Abuja an gano ta a wajen Shema Filling Station a Unguwar Gwari. Wanda ake zargin da satar Motar ya tsere da ganin ƴan sanda,” a cewar kakakin.

Advertisement

Ya ce motar tana hannun su kuma za a mika ta ga rundunar ƴan sandan Abuja.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending