Connect with us

News

Toshewar Magudanar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Matasa 4 A Kano

Published

on

FB IMG 1723570815626

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu matasa hudu, sakamakon fadawa cikin wata magudanar ruwa da ta cika a unguwar Zangon Kaya, da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, a sakamakon toshewar magudanar da ginin layin dogo ya haifar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 18 ga Yuli, 2025, da misalin karfe 1:48 na rana, bayan samun kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin mai suna Rabiu Yusif.

Toshewar Magudanar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Matasa 4 A Kano

A cewarsa, matasa biyu ne suka fara shiga cikin magudanar ruwan domin yin wanka, amma suka makale. Na uku ya shiga domin cetonsu, amma shima ya makale. Haka nan matashi na hudu ya shiga domin ceto su gaba ɗaya, shima ruwan ya cinye shi.

“Mutane mazauna yankin sun fitar da mutum biyu kafin isowar jami’anmu, daga nan kuma mu muka ciro sauran biyun daga cikin ruwan,” in ji ACFO Saminu.

Wadanda lamarin ya ritsa da su su ne Nasirudden Tasi’u, mai shekaru 25, Bashir Sani, mai shekaru 28, Yakubu Muhammad, mai shekaru 22, Usman Ubale, mai shekaru 26

Hukumar ta ce dukkan matasan an fitar da su cikin halin rashin numfashi, kuma daga bisani an tabbatar da mutuwarsu. Jami’an hukumar sun mika gawarwakin ga jami’in ‘yan sanda, SP Abdulkadir M. Albasu na ofishin ‘yan sanda na Dawanau, domin gudanar da bincike.

Advertisement

Binciken farko ya nuna cewa cikar ruwan ya samo asali ne daga ginin layin dogo da ya hana ruwan wucewa yadda ya kamata. Wannan kuwa ya janyo ruwan ya tara a magudanar da ba a kula da ita ba.

Hukumar kashe gobara ta shawarci iyaye da al’umma da su sanya ido sosai akan matasa, tare da kauce wa yin wanka a wuraren da ba su da kariya ko tsari, musamman a lokutan damina.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending