Connect with us

News

Kungiyar Ma’aikatan Wucin Gadi Ta Kalubalanci ICPC Kan Gurfanar da Shugaban KANSIEC

Published

on

images (2)

Wasu daga cikin ma’aikatan wucin gadi da suka yi aikin zaben kananan hukumomi a Jihar Kano sun bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) da ta nisanta kanta daga shiga harkokin siyasa.

Shugaban kungiyar ma’aikatan, Auwal Shuaibu, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Abuja, inda ya ce suna da shakku kan yadda ICPC ke shirin gurfanar da shugaban hukumar zabe ta jihar Kano da wasu jami’an hukumar a gaban kotu.

Advertisement

‎Martani Kan – Ziyarar Tinubu a Kano: Shaidar Ƙarfin Siyasar Sanata Barau a Arewacin Najeriya

A cewar Auwal Shuaibu, ICPC ta bayyana cewa za ta gurfanar da Farfesa Sani Lawan Malumfashi da wasu jami’ai biyu a ranar Litinin 21 ga watan Yuni, 2025.

Kungiyar ta ce tana ganin matakin yana da alaka da siyasa, inda ta zargi wasu ‘yan adawa da kitsa lamarin domin bata sunan shugaban hukumar zaben, musamman bayan yadda suka gaza hana gudanar da zaben kananan hukumomi a shekarar 2024.

Advertisement

Auwal ya ce, “An biya mu hakkokinmu a bainar jama’a ba tare da wata matsala ba. Zaben ma ya gudana cikin lumana da gaskiya.”

Kungiyar ta bukaci ICPC da ta yi bincikenta cikin gaskiya da adalci ba tare da nuna son rai ba ko bin ra’ayoyin wasu ‘yan siyasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending