News
Yaƙin Ukraine: Putin ya sauya tsarin duniya – amma ba yadda yake so ba
Mamayar da shugaba Vladimir Putin ya yi a Ukraine ta sauya duniya baki dayanta. Ana rayuwa a sabon karni mai cike da hadari, kwatankwacin shekarun cacar baka da zamanin da aka kawo karshen bangon Berlin.

Ba safai ake rayuwa a lokutan da aka yi wa tarihi hawan kawara ba, da tunanin abin da zai je ya komo, har kuma a fahimci halin da ake ciki.
A watan Nuwanbar 1989, ina tsaye cikin dusar kankara a dandalin Wenceslas da ke Prague, babban birnin kasar wanda a wancan lokacin ake kira Czechoslovakia. Ina kallon yadda ake shirin haifar da sabon karni na duniyarmu.
Al’ummar gabashin Turai ta yunkuro domin kare kanta da kuma kawo karshen mulkin danniya. An ruguza katangar Berlin, kana an samar da wani sabon yanki a Turai a wancan lokacin.
A birnin Prague, marubuci kuma mai bayyana sabanin ra’ayi, Vaclav Havel ya yi wa dandazon mutum 400,000 jawabi, daga farfajiyar wani gini mai hawa biyu. Zuwa yammacin wannan ranar aka raba gwamnatin kwamunusanci ta kasar da mulki, kuma cikin makonni Havel ya zama shugaban kasar karkashin tafarkin mulkin dimukradiyya.
Daga wannan lokacin na fara yin nazari kan yadda duniyar ke sauyawa, wanda lokaci ne mai cike da tarihi – inda akan idonka kana ganin yadda duniya ke sauyawa cikin sauri.
Shin sau nawa ne cikin tarihin Turai, tun bayan juyin juya halin Faransa aka samu irin wannan sauyin? Ina ganin kamar sau biyar haka ta taba faruwa. Wannan na shekarar 1989, shi ne karo na shida.
Sai dai irin wannan lokacin da ake sake samar da sabuwar duniya, yayin juyin juya halin da suka faru na baya-bayan nan da shugaba Putin ya kaddamar, wato na mamayar Ukraine ta amfani da karfin soji, shi ne ya dawo da zamanin baya da abubuwan da suka faru a shekarun da suka shude.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya bayyana wannan lokaci a matsayin mai matukar wahalarwa – yayin da sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Liz Truss ta ce wannan “gagarumin” yanayi na sauyi ne. Ta kuma ce zamanin yin sakaci ya wuce har abada.
- 1789: Juyin-juya halin Faransa. An kawo karshen mulkin mulaka’u, tare da samar da jamhuriya
- 1815: ‘Yan majalisar Vienna sun zana sabuwar da taswirar Turai, da daidaita rabon madafan iko, da kuma tabbatar da zaman lafiya a gwamman shekaru bayan yakin zamanin Napoleon
- 1848: Juyin-juya halin na masu sassauci a kasashen Turai wadanda suka kafa mulkin dimukradiyya
- 1919: Yarjejeniyar Versailles. Sabbin kasashe masu cin gashin kai sun maye gurbin tsofaffin dauloli
- 1945: Yalta – kasashe mafi karfin iko sun amince a raba Turai zuwa bangaren yammaci Turai da na yankin Soviet. Daga nan ne “labulen karfe” ya tsaga nahiyar gida biyu
- 1989: Dimukradiyya ta bayyana a tarayyar Soviet da kasashen gabashin Turai. Shekara biyu bayan nan tarayyar Soviet ta durkushe. Vladimir Putin ya kira lokacin “yanayi mafi muni a karni na 20”
-
baya-bayan nan, Quentin Sommerville daya daga cikin ma’aikatan BBC da ya goge wajen dauko rahotanni a wuraren da ake yaki, ya ce ruwan bama-baman da Rasha ta yi a birnin Kharkiv na Ukraine: “Idan ba ka san irin wannan dabarar yakin ba, to tabbas ba ka taba mai da hankali akan abin da ke faruwa a duniya ba ke nan.”
Alamu da shaidu sun dade da bayyana kan abin da Rasha ke son yi.
Shekaru 20 ke nan tun bayan da ya tura sojoji zuwa Georgia, tare da ikirarin yana taimakon ‘yan awaren kasar ne.
Daga bisani, ya aike da ‘yan leken asiri zuwa wasu biranen Birtaniya dauke da guba domin hallaka ‘yan Rasha da suka tserewa kasar.
A shekarar 2014, ya mamaye gabashin Ukraine, tare da mallakar yankin Crimea.
Duk da wannan, Jamus da yawancin kasashen Turai, sun yi biris tare da dauke ido saboda sun dogara ne da makamashi da iskar gas din da Rasha ke sayar musu.
Shekara guda bayan mamayar yankin Crimea, suka amince da gina wani dogon bututun da zai bunkasa safarar iskar gas tsakanin Rasha da kasashen Turai.
A Wani lamari da Liz Truss, ta bayyana a matsayar babbar matsalar da kasarta ke fuskanta.
Birtaniya ta zama tudun mun tsira inda Rasha ke adana kudadenta, tun zamanin Firaminista John Major.
Manyan attajiran Rasha sun tara biliyoyin daloli a Birtaniya, tare da sayen gidaje masu matukar tsada, da kuma jiragen sama, da mu’amala da manyan ‘yan siyasa da attajirai da bayar da tallafi ga kungiyoyin agaji.
Tambayoyi kalilan aka yi kan ta ina suke samun irin wadannan mahaukatan kudaden, kuma cikin lokaci kadan.
Da fari, ya yi amanna kasashen turai na cike da tarin matsaloli, ya shaida hakan a lokacin da aka samu rarrabuwar kawuna tsakaninsu. Kan zaben shugaba Donald Trump da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ya tabbatar da hasashen na shi.
Sai kuma tasowar masu ra’ayin sassauci a kasashen Poland da Hungary, hakan ya kara sanyawa ya samu kwanciyar hankalin cikar muradunsa.
A shekarar 1992, ‘yan asalin Sabiya sun kaddamar da yaki domin karyawa da kassara sabuwar kasar da ta samu ‘yancin kai, ko mu ce jaririya wato Bosnia. Sun yi ta musun cewa Bosnia ba ta da wani tushe na ta na kashin kai, sannan sun kafe cewa ba ta da wani cikakken tarihi da har za a bata gashin kai, sannan sun kafe tabbas wani bangare ne a kasar Sabiya.
Wannan shi ne ainahin kallon da Shugaba Vladmir Putin ke yi wa Ukraine.
